Tuesday, September 23, 2008

I'ITIKAFI

I'ITIKAFI

Dasunan Allah mai Rahama Mai Jinkai

Shine lazimtan masallaci da zama cikinsa da niyyan samun kusanci zuwa ga Allah. kuma malamai sunyi ittifak'I -wato sun hadu- akan cewa itikafi an shar'antashi kuma mustahabbi ne.

Tunatarwa: wasu mutane na kuskure ta yanda suke daukan cewa Itikafi, yakebanci manzan Allah ne Sallalahu Alaihi Wasallam shi kadai, wasu kuma suce hadisin Itikafi an shafe shi, wasu kuma suna dauka cewa Itikafi na dattawane ko akasin hakan, to duk wadannan kurakurai ne ba'a sha. Nana A'isha Allah yakara yarda agareta tace: (Lallai manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yanayin Itikafi a cikin goma na K'arshe na Ramadan har Allah yadauki ransa, sannan matansa sukayi Itikafi a bayansa) Bukhari. Ibn Hjar yace (Ba'a shafe hadisin ba kuma baya cikin abubuwan da suka kebanci ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam)fathul baari 4/272.

HUKUNCIN ITIKAFI

Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa mustahabbi ne.

Imamu Malik Yace: (Nayi tunani akan al'amarin Itikafi, da abinda yazo akansa, da yanda musulmai suka barshi, tareda cewa manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be kasance yabarshi ba, se naga cewa sun barshi ne saboda yanada wahala akansu.)

Imam Azzuhri Yace: (akwai mamaki a Al'amarin musulmi! Sun bar Itikafi, tareda cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, be barshi ba tunda yazo Madinah , har Allah madaukakin Sarki yadauka ransa.)

SHARUDDAN ITIKAFI

1. MUSULUNCI: baya inganta ga wanda ba musulmi ba.

2. HANKALI: mahaukaci baya itikafi, saboda koda ibada ta wajibi bata zama dole akansu ba, andaga alkalami akansu.

3. NIYYA: sharad'I ce ga dukkan ibadodi, kuma duk aikmin da babu niyya a cikinsa ba karbabbe bane.

4. MASALLACI: ga namiji dolene yayi a masallaci, amma mace kuma anyi sabani akanta, Malam SUHNUNU Yace: (nace ma ibnul K'asim: menene zancen Imamu Malik gameda Itikafin mace tayi amasallacin jama'a? se yace Na'am, yace: a zancen Malik tayi Itikafi a masallacin gidanta? Se yace: Hakan baya burgeni, ana itikafi ne a masallacin da'aka yishi dan Allah.) Mudawwana 1/295.

Sheikh Aminul Hajj yace: (amma yafi rinjayen dalili awurina shine mace tayi Itikafinta a gidanta, wato wurin da takebance shi tana sallah a cikinsa.

5. AZUMI: wasu daga cikin malamai sukace kada mutum yayi itikafi face yaname Azumi, an tambayi Ibnul K'asim: (shin anayin itikafi batare da azumi ba a cikin zancen Malik? Se yace: ba'ayi se da Azumi. Wasu kuma sukace anayi koda mutum beyi Azumi ba, Sukace wannan shine ra'ayi mafi rinjayen dalili, saboda Hadisi Umar ingantacce da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya Umarce shi da yayi itikafi yayin da yace masa yayi alwashin yin hakan a jahiliyya, kuma be ce masa yayi Azumi ba.

6. IZINI: dolene se miji yayi wa matarsa izini ko abinda ya mallaka na bawa ko baiwa, miji mace yana gida ne ko yayi tafiya dole tanemi izininsa, kuma idan yayi mata izini, to be kamata ya hanata ba kuma.

RUKUNNAN ITIKAFI

1. Zama a cikin Masallaci. 2. Nisantan Jima'I da abubuwan da zasu iya kaishi yin hakan. 3. Nisantar manyan laifuka. 4. Musulunci. 5. Hankali. 6. Tsarki daga Haila. Itikafi yana baci saboda rashin daya daga cikin wadannan.

ABUBUWAN DASUKE BATA ITIKAFI

1. FITA DAGA MASALLACI: baya halasta fita daga masallaci, In banda fita saboda: dan Biyan bukata kamar fitsari ko bayan gari, wankan janaba da na jumu'ah, cin abinci ko abin sha idan be iya ci ko sha a wurin da yake itikafi, idan yaji tsoron wuta ko sata kom rushewan gini, in aka fitar da shi da karfi, idan mace tayi haila da sharadin ta dawo da tayi tsarki, idan mijin mace yarasu ko yasake ta zata fita a mafi rinjayen zancen malamai biyu wasu sukace zata cigaba har seta kammala, fita saboda yin Umara, fita da mantuwa, idan yayi hauka ko suma.

2. YIN JIMA'I: saboda Allah yace: (kuma kada ku sadu dasu, alhalin kuna masu Itikafi a cikin masallatai…) Sur.Baqarah-186. haka sun bantan mace da sha'awa.

3. YIN RIDDA:wato fita daga musulunci

4. YIN MANYAN LAIFUKA: kamar yin zina da sata acikin itikafi, wanda mutane suna sakaci da daukan abin wani ko da kadan kuwa se a kiyaye.

5. YIN HAUKA KO SUMA: yana bata itikafi se dai idan yasami lafiya ko ya farfad'o to se yacigaba.

6. HAILA: idan mace tayi haila itikafinta ya baci, amma idan tayi tsarki se ta cigaba, na bayan be baciba.

ABUBUWAN DA BA'ASO GAME ITIKAFI

Ba'aso me itikafi ya shagaltu da abinda ba ambaton Allah ba, da kuma abinda ba dolene ba.

1. jayayya. 2. zagi damaganganun banza. 3. Yin giiba da Annamimanci. 4. Kallon abinda yake haramun. 5. Rashin yin magana gaba daya tun daga safe har dare da sunan bauta.

Tunatarwa: wasu daga cikin daliban ilimi se kaga suna zuwa itikafi da wasu littafai na karatunsu suna yin muraja'a, ba haramun bane amma kamata yayi tunda kwanakine yan kadan a cikin shekara, meze sa bazakayi hakuriba, sauran kwanakin shekara kayi acikinsu.

ABUBUWAN DASUKA HALASTA GAME ITIKAFI

1. Yin wanka da canza kaya, da sanya kayan da yakeso.

2. Cin Abinci da Shan Abin Sha a cikin masallaci.

3. Yin magan da yan uwa, amma ba'ason yawaita surutu da mutane.

4.Ya nemi Aure ko a daura masa Aure.

5. Yin Aski da yanke Farce.

6. Sanya turare.

ABUBUWAN DA SUKE MUSTAHABBI GA ME ITIKAFI

1. Mustahabbi ne ga me itikafi, yakafa tanti da ze kangeshi daga jama'a, inbe samu ba se ya lazimce wurin da babu jama'a ta yanda baze barshi ba seda larura.

2. kiyaye yin Sallah cikin jama'a, da nafiloli.

3. Yawan karatun alk'ur'ani, da rashin shagaltuwa da abinda ba ruwa.

4. Yawan ambaton Allah, zikiri, da tasbihi.

5. Yin azumi a cikin wantan da ba ramadan, ga wanda zeyi itikafi da rana.

6. Yawan yin kokari wajen d'a'a.

MAFI KARANCIN ITIKAFI DA MAFI YAWANSA

Itikafin neman lada baya da kad'an ko mafi yawa, se dai wanda yayi Itikafi a goman k'arshe na Azumin kada ya fita se idan anga watan Sallah wato Shawwal, malamai sun hadu akan cewa baya da mafi yawa, amma sunyi maganganu akan karancinsa, wasu sukace mafi karancinsa Sa'a, wasu sukace Yini daya da dare, wasu sukace kwana goma.

Imamul k'urtabi yace: ( mafi karancin itikafi a wajen Malik, da Abu Hanifa, dare da yini….)

YAUSHE AKE SHIGA ITIKAFI KUMA YAUSHE AKE FITA

A. Shiga wajen itikafi:akwai zancen malamai guda biyu:

1. Shiga bayan sallar Asubahin ranar Ashirin da d'aya na Ramadan, saboda hadisin Nana A'isha Allah yakara mata yarda tace: (Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam idan ze shiga itikafi yana yin sallar Asubahi, sannan se yashiga wurin itikafinsa) Bukhari. kuma wannan shine mafi rinjayen dalili. Kuma mazhabinAhmad da Laith da Ishak'.

2. Shiga kafin rana r daren Ashirin da d'aya ta fad'i, wannan shine mazhabin Malamai hud'u

B. Fita daga itikafi: Ana fita daga wurin itikafi bayan ganin watan sallah, wasu kuma sukace mustahabbine ya bari har yayi sallar idi sannan ya tafi.

SIRRIN DA YAKE CIKIN I'ITIKAFI

Bauta tana da sirruka da hikimomi masu yawa, saboda ayyuka gaba daya, makewayansu itace Zuciya, kamar yanda Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace (..Kusaurara! lallai acikin jiki akwai wata tsoka wanda idan ta gyaru, to dukkan sauran jiki ya gyaru, kuma idan ta bace, to dukkan Sauran jiki ya baci, ku saurara! Itace zuciya.) Bukhari da Muslim.

To in muka duba zamuga cewa mafi yawan abubuwan da suke bata zuciya, sune sha'awan cin abinci da abin sha da saduwa da Iyali da Zancen da ba na dole ba, da barcin da ba na dole ba, da abokai da basu da wata fa'ida da sauran abubuwa dasuke kawar da zuciya daga yin abinda yake biyayya ne ga Allah, se Allah ya Shar'anta wasu abubuwa na lada da zasukare zuciya daga rud'ani da shagaltuwa daga ambaton Allah, kamar Azumi wanda yake hana mutum cin abinci da abin Sha da Saduwa da Iyali da rana. To wannan hanuwan daga wadannan abubuwan jin dadi, shine yake karfafa alak'a tsakanin mutum da Ubangijinsa, da fuskantar dashi ga Lahira, kena Azumi garkuwa ce datake kare zuciya daga abubuwan sha'awa da suke kawar da mutum daga yin biyayya ga Allah, duk da hanine wanda yake matsakaici saboda an halasta wa mutum wadannan abubuwa a cikin dare.

To haka shima Itikafi yanada Sirri me girma, shine Kare mutum daga yawan cakud'a da jama'a, da yawan magana, saboda me Itikafi yana shagaltuwane da karatun Alk'ur'ani da Tsayuwa –wato yin sallah- da Zikiri da yawan yin Addu'a da makamantansu, haka kuma akwai kariya daga yawan barci, tunda yazo ibada ne ba barci ba, to wadannan abubuwa barinsu shike kara sa zuciya ta fuskanci Allah.

ABUBUWAN TUNATARWA

* Wasu daga cikin malamai sun tafi akan cewa ba'ayin Itikafi se a masallatai guda Uku kamar yadda yazo a cikin Hadisi, na hani akan yin Itikafi a masallatan da basuba, manzan Allah Sallalahu Alaihi Waasallam yace (Babu Itikafi face a masallatai guda uku) imamu Tahawi. -Wato masallacin Harami wato Ka'abah da masallacin Madinah da masallacin Aqsa wato Kudus-, Malamai suka fassara shi da cewa hani ne na yin alwashin yin Itikafi a wani masallaci da tafiya zuwa gareshi saboda hakan se a wadannan masallatan kadai ya halatta, ayi hakan saboda duk malaman mazhabobi Hud'u sun hadu akan cewa ya halatta ayi a kowani masallacin Juma'a.

* wasu sukan bar ayyukansu na wajibi saboda suyi Itikafi, to yin hakan kuskure ne saboda shi Itikafi sunna ce, saboda haka ba'a barin abinda yake wajibi saboda Sunnah.

Ya Allah Ka Karba mana dukkan Ayyukanmu a cikin Watan Ramadana kasa Muna cikin Bayinka Yantattu dag Wuta kuma kadatarmu da daren Lailatul K'adari. Amiin

No comments: