Tuesday, September 23, 2008

Wata Me Tarihi

Yin Bushara da Azumin Ramadan

Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana yima Sahabbansa Bushara da shifa watan Ramadankamar yadda Imamu Ahmad da Imamu Nasa'I suka kawo Hadisin da Abu Hurairah ya ruwaito daga Manzan Allah Sallalahu Alaihi Wasallam yace manzan Allah yakasance yanayiwa Sahabbansa Bushara "Hak'ik'a watan Ramadana mai albarka yazo maku, Allah ya wajabta maku Azumtansa, Ana bud'e kofofin Aljanna acikinsa kuma ana kulle kofofin Wuta , kuma ana D'aure Shaidanu acikinsa, akwai dare da tafi wata dubu acikinsa…………"

Watan Ramadan Yanada Wadansu Falala:

1. Watan da'aka Saukarda Alk'ur'ani 2. watan Taraawih da Tahajjud. 3. Watan Tuba da Kankare Zunubai. 4. watan Daure Shaid'anu. 5. watan da'ake kulle kofofin Wuta. 6. watan da'ake bud'e kofofin Aljanna. 7. watan kyauta da Ihsani. 8. watan da'ake y'antawa daga wuta. 9. watan Lailatul K'adr. 10. watajnAddu'a. 11. watan Jihadi. 12. watan da'ake nunka Lada acikinsa. 13. watan Hak'uri da Godiya.

Wata Me Tarihi

Watan Ramadan Watane me Tarihi acikin Musulunci wanda acikinsa aka Samu da yawa daga cikin Nasarorin yak'i da Kafirai. Gasu kamar haka:

Shekar Ta Farko: acikin Ramadan aka aika Sariyya ta farko k'ark'ashin jagorancin Hamza bn Abdulmutallib, se Sariyyan Ubaidah binil Harith, domin sanya tsoro acikin zukatan Kafirai.

Shekar Ta Biyu: acikin Sha bakwai ga Ramadan akayi Yak'in Badar Alkubra.

Shekar Ta Uku: a cikin Ramadan manzan Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya Shirya Runduna a madinah domin su hana mushrikai dasuke son daukan Fansan Yak'in Badr.

Shekar Ta Biyar: Shiryawa Yak'in Khandaq, anyi yak'in ne acikin watan Shawwal wato watan Sallah kamar yanda Imamu bnil Qayyim yace Sun shirya mashi da wata d'aya wato suna hakk'a ganuwa.

Shekar Ta Shida: Sariyyan Gaalib bin Abdullah wanda ta kunshi mutum da'ri da talatin wanda sukayi nasara akan bani Abdullahi bn tha'alabah.

Shekar Ta Takwas: Bud'e Makkah acikin Ashirin ga Ramadan Allah ya daukaka Addininsa da manzansa da muminaikuma ya tseratar da Dakinsa me alfarma daga Hannun Mushrikan K'uraishawa, manzan Allah Sallalalhu Alaihi Wasallalm ya Shigeta tare dashi akwai Sojojin Musulunci dubu Goma.

Shekar Ta Tara: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shi da Sahabbaqnsa suka dawo daga Ykin Tabuka.

Shekar Ta Sha Uku: Yak'in Buwaib yakasance cikin ramadan a wuri da ake kira Buwaib kusa da kufa a yau acikin k'asar Iraq inda Farisawa karkashin jagorancin Mahran da musulmai Karkashin Jagorancin Almuthanna bin Harithah wanda yaki me matikar muni ya afku daga karshe Allah yaba musulmai nasara, an kashe da dama daga cikin musulmi, sukuma Farisawa tsakanin wanda aka kashe da wanda suka fad'a cikin ruwan Furat wajen gudu kimanin Dubu D'ari kuma aka samu Ganima me yawa, daganan ne aka karya Lagwan Farisawa. Sannan se Bud'e Garin Nuuba, a kudancin masarkarkashin Jagorancin Abdullahi bin Sa'ad bin Abi Sarah, wandA hakan ya bud'e kofa ga muslunci wajen Yad'uwa a garuruwa da yawa.

Shekar Ta 53: Bud'e TsibirinRuuds, a karkashin Junadah bn Abi Umaiyah.

Shekar Ta 67: Aka Gusar da daular Mukhtar Athak'afi wanda aka kashe a sha hud'u ga ramadan karkashin jagorancin Gwamnan Basra Mus'ab bini Zubair.

Shekar Ta 91: Bud'e Andalus a hannun D'arik' bin Yazid bawan Musa dan Nusair sannan se Yak'in D'urif, musa bin Nusair ya aika wani mutum daga cikin K'abilar Bar-Bar ana kiransa D'uraif da mutane dari hudu da dawakai dari, inda suka tafi suka kai farmaki a gefen tekun Andalus kuma suka dawo da nasara.

Shekar Ta 102: Musulmai suka bud'e Faransa bayan sun kafu a Andalus wato Spain kenan, se suka fara yakan Arewaci da yak'I abayan duwatsun pranis wanda suke tsakaninn Andalus da Faransa wanda da yawa daga cikin dakaru suka jagoranta. Acikin dan wannan gajeren lokaci baze yiwu mu iya ambatan duk yakin da'akayi cikin Ramadana ba ko bayanai sosai gameda hakan, kawai munso bayyana wasu daga cikine kawai dan nuna muhimmancin wannan wata da tarihinsa wajen musulmi.

No comments: