Wednesday, November 21, 2007

ABUBUWAN DA'AKA HALASTA MA ME AZUMI

ABUBUWAN DA'AKA HALASTA MA ME AZUMI SUNE KAMAR HAKA:


1. Shiga cikin Ruwa da yin nitso aciki da sanyaya jiki saboda tsananin zafi, Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance : ( "Yana zuba ruwa akansa, yana me Azumi saboda k�ishi ko saboda Zafi" Ahmad da Abu Dawud).

2. Yawayi gari yana me janaba ya halasta, Saboda fadin Nana A'isha Allah ya kara mata yarda :

( "Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yana wayan gari da janba yana Azumi sannan yayi wanka " Bukhari da muslim). wato acikin Azumin Ramadan.

3. Ci da Sha da Jima�i cikin dare har zuwa lakacin fitowar alfijir, Saboda fadin Ma�aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: ("Lallai Bilal yana kiran Sallah da dare, to kuci ku sha har se dan umm maktum ya kira sallah " Bukhari da muslim). Wato bilal nayin kira na farko shikuma yanayin kira na biyu.

4. Me jinin Haila da me jinin Bik'i, idan jinin ya yanke mata cikin dare ya halasta su jinkirta wankan har zuwa Asubahi, kuma su wayi gari da Azuminsu sannan suyi wanka kafin suyi Sallah.

5. Cin Aswaki a farkon Yini da karshensa, saboda cin Aswaki mustabbine kuma babu wani dalili da yanuna cewa za�ayi shi a wani lokaci banda wani, wannan shine mazhabin mafi yawan malamai.

6. Yin tafiya dan wata bukata ta halas koda tafiyan zatasahi shan ruwa.

7. Yin magani kowani Irii idan matukar baze tafi cikinsa ba kamar yin alluran da bata abinci bace.

8. Tauna abinci da d'and'ana shi da sharadin babu abinda zewuce ciki.

9. Yin amfani da turare da Shakan kanshi me dad'i.

1 comment:

MUHAMMAD YAHAYA BARMA said...

Bam - Bamci tsakanin Wankan Janaba da Wankan tsabta

DAGA: Shafin: www.islamtoday.net

Tanbaya:

Menene Bambanci tsakanin Wankan Janaba da Wankan tsabta? wajen isarwarsu daga alwala ko rashinta? kuma shin yin Alwala sharadi ne game da wankan tsabta? dakuma wajen yin niyya, Allah yasaka maku da Alkhairi.

Mai Me bada Amsa:

Dr. Sulaiman bin Wa'il Attuwaijiri, Mamba a kwamitin malamai na Jami'ar Ummul Qura dake makkah.

Rana: 27-6-1424 A.H.

Amsa: Wankan Janaba, wankane dayake dauke Hadasi babba, ita kuma Alwala tana dauke hadasi ne wanda yake karami, shi kuma wanka na tsabta, ba ya dauke wani hadasi, to da mutum zeyi niyyan wanka, wato bana janaba ba, kawai yayi wankan tsabta ne ko wankan juma'a, se yayi nufin dauke hadasi karami dashi wato alwala, to be isar masa ba, domin a wankan babu nufin dauke hadasi a cikinsa, Allah madaukakin Sarki kuma yana cewa "kuma idan kun kasance masu janaba to kuyi tsarki" to alwala tana shiga cikin wankan janaba wajen dauke hadasi, se hadasi karani ya shiga cikin hadasi babba, wajen daukewa da abinda ze halarta sallah, amma shi kuma wanka na tsabta, badauke hadasi yakeyi ba saboda haka be idarwa gameda alwala, myazama dole yayi alwala da farillanta da jerantawa a gabbai. Allah shine mafi sani.

MASHA ALLAH YASAKA DA ALKAIRI

MUHAMMAD YAHAYA BARMA
KANO NIGERIA