Tuesday, November 20, 2007

KWANAKIN DA AZUMI YAKE HARAMUN A CIKINSU

KWANAKIN DA’AKA HARAMTA YIN AZUMI CIKINSU

1. Ranakun Idi guda biyu, Idi babba da Idi Krama, Saboda Fadin Umar dan khattab Allah yakara masa yarda: (“Lallai wadannan kwanaki guda biyu manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: yahana Azumi a cikinsu, Ranar da kuke shan daga Azuminku, da ranar da kuke ci daga yankanku” Muslim).
2. Kwanaki uku na shanyan nama (Ayyamut-tashreeq) wato kwanakin babban sallah guda uku, Sha daya da sha biyu da sha uku ga watan zulhijjah, Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: ya aiki Abdullahi dan Huzafah Allah yakara masa yarda yana kewayawa a muna yana cewa: (“kada kuyi Azumin wadannan kwanakin, domin su ranaku ne na cin da sha da ambaton Allah madaukakin sarki” Ahmad). Amma wannan banda mahajjaci, meyin tamattu’i da meyin Qiraani idan beda Hadaya.
3. Ranakun da mace take Haila da Bik’i, Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: a gameda hakkin mace, yace: (“Ba idan tayi haila bata sallah ba? To wannan shine tawaya -rashin cikan- addininta” Bukhari). Kuma malamai sunyi Ijma’i wato basuyi sabani ba akan bacin Azumin me haila da me bik’i.
4. Azumin mace idan mijinta na gari se idan ta nemi Izininsa, Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: ( "Kada mace tayi Azumi alhali mijinta yana nan se dai idan da Izininsa amma banda Azumin ramadan" Bukhari da muslim).

1 comment:

Unknown said...

Loved your site, Lee! Thanks for sharing Kami menyediakan berbagai macam obat seperti Obat kondiloma , Kencing Nanah , Wasir , Sipilis , Herpes , Diabetes