Tuesday, November 20, 2007

Azumin Neman Lada (wato Nafila)

AZUMIN NEMAN LADA (NAFILA)

Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kwadaitar da yin wadannan Azumin kamar haka:

1. Azumin kwana shida na watan Shawwal –watan salla karama- Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: ( “Duk wanda yayi Azumi Ramadan, sannan ya bisu da Azumi Shida na Shawwal..... za’a bashi lada kamar na wanda yayi shekara yana Azumi ba hutawa.
2. Azumin Ranakun Litin da Alhamis, dan Fadin Abu Hurairah Allah yakara masa yarda yace: (manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yafi yawan yin Azumi a Litinin da Alhamis, se akace masa wato aka tambayeshi dalilan dayasa yake Azumtansu, se yace: (“Ana bijiro da ayyuka akowace ranar litinin da Alhamis, se Allah ya gafartama kowani musulmi ko kowani mumini in banda masu gaba da juna, se yace: kujinkirta masu” Ahmad).
3. Azumin kwana uku a cikin kowani wata, Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: ( “Yin Azumin kwana uku a cikin kowani wata: Azumin Shekara, sune kwanakin biidh safiyan Sha uku, sha hudu,sha biyar” Nasa’i ).
4. Azumin ranakun farko na watan zul-hijjah, Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: ( “babu wasu kwanakin da Allah madaukakin sarki yafison Ayyukan Alkhairi a cikinsu kaman wadannan kwanank-wato kwanakin zulhijjah- sukace ya manzan Allah koda Jihadi akan tafarkin Allah? Yace koda Jihadi akan tafarkin Allah in banda kawai mutumin daya fita da kansa da dukiyarsa, sannan bedawo da komai ba” Bukhari). Wato kudin sun kare kuma yayi shahada. Kuma ranar da tafisu duka itace ranar Arafah, wato ranar tara ga watan zulhijjah, ga wanda ba mahajjaci ba Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: (“Yin Azumin ranar Arafa yana kankare zunubban shekaru biyu, wadda ta wuce da me zuwa” Muslim). amma k'ananan zunubai ake nufi a Hadisin, manayan laifuka kuwa sedai tuba ke kankaresu.
5. Azumin Watan Muharram, Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: yayinda aka tambayeshi: wani Azumine yafi falala bayan Ramadan? Yace: (“watan Allah dakuke kira muharram” Muslim).
6. Azumin Ranar Ashura, shine ranar goma ga wata, Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: (“ kuyi Azumin ranar Ashura, yana kankare Shekaran data gabata” Muslim). Kuma Mustahabbi ne ayi Azumin ranar tara ga wata hade da goma saboda sab’awa Yahudawa da Nasara, domin sanda akacewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam gameda Azumin Ashura cewa yayi: “Rana ce da Yahudawa da Nasra suke girmamata” Se yace: ( “Idan Allah ya kaimu shekara mezuwa zanyi Azumin tara” shekaran bata zoba anzan Allah ya rasu) Muslim.

No comments: