Tuesday, November 20, 2007

RANAKUN DA'AKA HANA YIN AZUMI A CIKINSU

RANAKUN DA AKA KYAMACI YIN AZUMI CIKINSU (KARHANCI)

1. Yin Azumin Ranar Arafa ga mahajjaci wanda yake tsayuwan Arafa, Saboda Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: (“ Ranar Arafa da Ranar yanka –wato layya-, da kwanakin Shanya nama –wato kwanakin idi uku- Idinmu ne mu musulmai, kuma su kwanakin ci ne da sha” Abu dawud Tirmidhi).
2. Yin Azumin Ranar juma’a ita kad’ai, Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: (“ kada kuyi Azumin ranar juma’ah ita kadai, sedai kafinta da rana daya ko bayanta da rana daya” Bukhari da muslim).
3. Yin Azumin Ranar Asabar ita kadai, Saboda Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: ( “kada kuyi Azumi ranar Asabar, se wanda aka wajabta maku ,idan da d’aya daga cikinku besami komaiba se bawon Inabi ko itacen bishiya to ya tattaunashi” Ahmad da Abu Dawud).
4. Azumin Shekara: Shine mutum yayi Azumin Shekara gaba daya ba tare da shan ruwa ba , Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: (“Babu Azumi ga wanda yayi Azumin shekara” Bukhari da muslim). da Fadansa:
5. Zarcewa da Azumi kwana biyu a jere ko fiye da haka da gangan batare da ya sha ruwa ba, shine abinda ake kira da wisaali, Saboda Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: (“Ina kashedin ku dayin wisali” Bukhari da muslim). Da fadansa: (“Kada ku zarce –wato dayin Azumi- duk wanda yakeso yazarce, cikinku to ya zarce zuwa lokacin Sahur” Bukhari).
6. Azumin Ranar shakka, itace ranar talatin ga watan sha’aban saboda Fadin Ammar bin Yasir Allah yakara masa yarda: (“Duk wanda yayi Azumin ranar da ake shakka to hakika ya sabama Abul-qasim, Sallallahu Alaihi Wasallam” Abu Dawud da Tirmidhi). Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: (“kada kurigayi ramadana da Azumin kwana daya k kwana biyu in banda mutumin da yakasance yanayin wani Azumi to se ya Azumceshi” Muslim).

No comments: